Wani matashi mai suna Muhammadu ya ce a yanzu rayuwarsa ta canza ta hanyar koyon sana’ar da ya yi a wajen Alhaji Aminu Bush “Farko lokacin da na zo wajensa, da sunan maula na zo amma sai ya nuna mani cewa wannan ba dabi’a bace mai kyau. In koyi sana’a ita ce hanya sahihiya. Nan take dai na nuna masa ina son inyi tukin mota ne, sai ya hada ni da wani daga cikin direbobin da suke yi masa aiki. Allah cikin ikonsa a yau nima na koyar da mutun uku wadanda kuma kowane yana jan motar kuma yana cin gashin kansa.”
Malam Muhammadu ya kara da cewa a iya saninsa bai iya cewa ga yawan matasan da suke cin abinci ta fuskar mota a karkashin wannan mutun “Wani abin ban mamaki ga Oga Bush shi ne, shi zai sa a koya maka tukin motar kuma shi ne zai baka motar da za ka ci gaba da aiki da ita kuma ba tare da ya kayyade maka irin aikin da za ka yi da ita ba muddin baka saba doka ba. Kuma ina tabbatar maka da cewa, ni dai bai taba cewa in bashi ko sisi ba sabanin ikayar da muka yi ta aiki. Ina zuwa Kano, Kaduna har zuwa Legas. Kuma fa ba ni kadai ke wannan ba. Kuma mafi yawan motocin da muke aiki da su nashi ne, in kuma gyara ya samu mu kai garejin shi ayi mana gyaran,” inji Muhammadu.
Shi kuwa Malam Rabi’u daya daga cikin kanukawan da suke aiki a garejin da shi Alhaji Aminu Bush ya bude ya ce “Gaskiya da za a samu mutane irinsu Alhaji, da maganar zaman banza ga matasa ta kare balle har su shiga cikin mugayen halaye. Mu dai a nan duk da bani ne shugaba ba, zan iya cewa babu wani mutun da ke aiki a nan da zai ce ya ga fuskar Alhaji ta canza ko don anyi wani abu ba daidai ba, in ma an nufe shi da wata magana sai ya ce aje wajen mai kula da sashen da masu maganar suke domin duk wani sashe na gyaran mota akwai shi acikin wannan gareji. Kuma bai hana mu kawo aiki daga waje mu yi ba. Hasali ma in kaga yana fada to ya same ku haka nan zaune babu wani aiki. Anan ne fa ko babu aiki sai ya kawo maku wani aikin ku je ku yi”.
Wani matashin wanda bai wuce shekara 17 zuwa 18 ba mai suna Abubakar da Wakilin Aminiya ya lura yana ta kokarin kwance wata kusa a wani inji, inda ya ce mako biyuke nan da ya fara aiki an wajen, kuma yana makarantar Sakandire ne “Ni na kawo kai na nan domin in koyi kanukanci don in dogara da kaina kuma in zamo ina da wata sana’a ta hannu saboda nan gaba”.
Ita ma wata mata mai sayar da abinci a bakin kofar garejin ta ce “Babban ci gaban da na samu shi ne na samun muhalli nawa na kaina. Yarana biyu marayu a yanzu in ka gansu ba zaka taba cewa marayu ne ba. Kuma duk sanadiyar wannan sana’a da nake yi a nan. Akwai wata rana da ba zan mance ba ga wannan bawan Allah Alhaji Aminu na shiga wani hali da jari na ya kare na yi kamar kwana uku ban fito ba, kawai sai ga wani ya zo ya ce yana kirana, ban tambaye shi ba kuma ban kuma ce a fada masa ga halin da nake ciki ba, ashe ya lura na bar fitowa kuma ya ji dalili, sai gashi ya bani buhun Shinkafa biyu da kwalin Taliy kyauta. Wannan abin har abada ba zan manta da shi ba. Iyakar matsalar da nake fuskanta bai wuce na gina rumfa ba, ita ma na gamsu da bayanin da aka yi mani na rashin isasshen wuri,” inji ta.
Da Aminiya ta tuntubi Alhaji Aminu Bush don jin ta bakinsa akan irin wannan namijin kokari da yake yi, cewa ya yi “A matsayina na matashi na fuskanci kalubalen rayuwa iri-iri domin ganin na dogara da kaina, na kuma ga irin halin da na samu kaina a baya kafin in zama abin da na zama, wannan ne yasa na rika rokon Allah Ya bani dama in rika taimakawa matasa domin su dogara da kansu. Hakika na lura da cewa idan matashi daya ya koyi sana’a to tamkar al’umma ce suka koya domin matasa ‘yan-uwansa za su yi koya.
Alhaji Aminu ya ce ba zai manta da wani abinda wani uban gidansa ya yi masa ba a lokacin da yake cikin gwagwarmaya inda ya ce “Wannan uban gida nawa wanda yake nan gabanka shi ne ya fara sayar mani da motarsa domin in jaraba kasuwanci da ita, kuma sai ince tukuici ne na bada. Ina iya cewa wannan na daya daga cikin irin abubuwan da ba zan manta ba kuma wannan yasa na kara sanin muhimmancin mota a wajen harkar kasuwanci,” inji shi.
“Ina ganin idan mutane musamman matasa za su rik kasuwanci ko sana’a sannan ga ilmi, to sai an wayi gari Jihar Katsina ta bayar da mamaki. Kaga za a kafa kanfanoni a jihar.”
A karshe matashin ya yi kira ga ‘yan uwansa da su hada kai domin tunkarar duk wata matsalar da ka iya taso masu, sannan ya shawarci gwamnati da ta rungumi ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu domin da haka sauran kasashe suka ci gaba