✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Kowace gwamnati kan zarge mu – Amnesty

Aminiya ta tattauna da Kakakin Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty reshen Najeriya, Isa Sanusi kan wannan batu: A kwanan nan ne Fadar Shugaban…

Aminiya ta tattauna da Kakakin Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty reshen Najeriya, Isa Sanusi kan wannan batu:

A kwanan nan ne Fadar Shugaban Kasa ta nuna korafi a kan kungiyarku ta Amnesty game da rahoton da kuka fitar tana zargin cewa akwai wata manufa ta raba kan ’yan kasa da kuke da ita. Yaya batun yake?

Mu dai abin da muka yi shi ne, mun shafe shekara 3 muna gudanar da bincike kama daga watan Junairu na shekarar 2016 zuwa watan Oktoba na bana a kan rigimar da ke ta aukuwa a tsakanin makiyaya da manoma a sassan Najeriya, inda rikicin ya fi kamari a jihohin Filato da Benuwai da Kaduna da Zamfara da wasu karin jihohi kamar Taraba da Adamawa. Mun yi bincike sannan muka gano cewa an kashe akalla mutum 3,641 a wadannan shekaru. Mutane da yawa sun mace alkaluman da muka fitar sun gaza hakikanin adadin wadanda aka kashen. Sai dai mu muna amfani ne da shaida. Ba mu yi wannan abin ba don raba kan kasa kamar yadda gwamnati ta yi zargi, illa don mu nuna muhimmancin ran dan Adam da nufin a yi gyara.

Idan  suna da hujja ta akasin haka to sai su fito da ita Allah Ya tona mana asiri kowa ya gane abin da ake zarginmu ya tabbata sai a hukunta mu. Sai dai ba komai ba ne illa maganar nan ne da ake cewa shure-shure ne ba ta hana mutuwa. Yanzu na ba ka misali, a lokacin da aka sanar da bacewar Janar Idris Muhammad Alkali (Allah Ya jikansa), wanda aka kashe a Jihar Filato, ka ga da sojoji suka sa kansu sai da suka gano inda gawarsa take, aka dauko ta aka yi mata sutura aka binne. Wannan ya nuna sojojin Najeriya suna da kwarewa da kayan aiki. To irin wannan zakewa ne muke son su nuna idan an kashe talaka a yankin karkara a Zamfara ko a Filato ko a Benuwai.

Takaita bincikenku a iya shekaru 3 da suka gabata da fitar da rahoton a daidai lokacin da aka fara kamfe din zabe, ya bai wa gwamnati damar zargin cewa akwai siyasa a cikin lamarin. Me za ka ce?

Waccan gwamnatin da ta gabata ma irin wannan zargi ta yi a kanmu. Sannan wani abu da zan so ka sani shi ne, a cikin jami’an wannan gwamnatin akwai wadanda a lokacin da Goodluck Jonathan ke mulki sun zo wajenmu sun yi korafi cewa ana musguna musu ana yi musu bita-da-kulli, mu muka tashi muka kare hakkinsu. Sannan waccan gwamnatin ta zarge mu da goya wa Buhari baya. Amma yanzu don su ke mulkin idan mun yi magana a kan kare hakkin jama’a sai su ce muna son mu farraka kasa? Mun sani a addinin Musulunci ana ba mu tarihin sahabbai irin su Sayyidina Umar, wadanda koda kyanwa ce ta mutu kuka suke yi suna tunanin Allah zai tambaye su. Amma kana mulki a kashe mutum 3,641 a shekara 3, ana gaya maka bai kamata ba, ba daidai ba ne, ya kamata ka gyara tafiyarka, amma sai ka ce ana yi maka siyasa, shin wace irin rayuwa ce wannan?

To ku me ya sa sai yanzu da za a fara zabe kuka fitar da binciken naku?

Wannan rahoto da ka ga muka fitar shekara 3 muka yi muna yin bincike a kai kamar yadda na yi bayani, mun so mu kaddamar da shi tun a  watan Agusta amma sakamakon yadda kashe-kashen ke karuwa, dole ta sa muka jinkirta tare da tabbatar da cewa duk abin da muka fitar muna da hujja a kai ta hanyar tabbatar da diddigi. Wadansu ma sun bukaci mu jinkirta har zuwa watan Janairu amma muka ce a’a, watan Janairu ya yi kusa da zabe kuma mu ba ’yan siyasa ba ne. Kai dai dan Adam ba ka iya masa, duk abin da ka yi sai ya nemi abin da zai dora maka. Sannan mu ba ’yan kwangila ba ne, ba mu kuma ce gwamnati ta ba mu rijiyar mai ba, ko mu je wajen wani mai kudi mu ce ya taimaka mana, to mai zai sa mu shiga harkar siyasa? Ka sani ita wannan kungiyar an kafa ta ce tun 1961 tare da ofisoshi a kasashe 159 a yanzu haka. Maganganun da muke fada a kan Shugaban Amurka Donald Trump da a kan Buhari ne muke fadarsu da Allah ne Ya san abin da za a yi mana. Idan abin da muke yi ba gaskiya ba ne, gwamnati na da kwararru su je su yi bincike a kai. Mu ba kotu ba ce duk abin da muka yi bincike muna gabatar da shi ne a matsayin zargi da nufin a tantance idan gaskiya ne a zantar da hukunci a kan masu laifi, idan karya ce a karyata mu. Amma maimakon haka sai a rika yin wasu barazana, to wannan ba zai hana mu ci gaba da yin aikinmu ba.

Kai da Shugaban Kwamitin Amintattu na wannan kungiyar ku ne sanannun muryoyi a nan Arewa, inda wadansu ke maku zargin cewa akidarku ta addinin Shi’a ke tasiri a kan korafe-korafen da kuke yi a kan wannan gwamnati, shin me za ka ce?

Wannan ba gaskiya ba ce. Mu dai mu ne masu yin bayani a Hausa shi ya sa aka fi saninmu, su ma ai sauran haka suke yi a bangaren Ingilshi. Amma abin da nake son jama’a su mai da hankalinsu a kai shi ne, su duba asarar rayuka da ake yi ba akidar mutum ba. Ba yadda za ka bar akidarka ta yi tasiri a kan aikinka da kake yi saboda kai na kowa ne. Ai kai dan jarida ne kuma ko wanda bai yarda akwai Allah ba ma za ka yi aiki a kansa. Batun akida daban aiki daban. Kai dai mutane ba ka raba su da magana, ai kafin in fara aiki a nan, a BBC nake aiki, shin me ya sa ba a taba kawo zargin ba a lokacin da nake aiki a wajen? A lokacin idan muka yi magana a kan Gwamnatin Goodluck Jonathan a kan wani zargi, ai ire-iren masu wannan korafi a yanzu dadi suke ji. Misali guda shi ne rahotanni da muka yi a kan kashe ’yan Shi’a a lokacin ai yaba mana suka yi. Amma a yanzu da aka kashe adadin da ya zarce na lokacin, idan muka yi magana sai a ce ai saboda muna cikinsu ne? To idan muka yi a kan ’yan Biyafra ma sai a ce mu ’yan Biyafra ne ke nan? Ya kamata mutane su rika jin tsoron Allah.

A karshe gwamnati ta ce wannan yaki da take yi da ta’addanci tana yin sa ne da bangarori biyu wato ’yan Boko Haram a daji, sai kuma ku kungiyoyin kare hakkin jama’a a cikin gari, me za ka ce?

To mu dai da muke wannan aiki ’yan Najeriya ne mu, kuma ba mu da wata kasa sai kasar nan. A nan muke zaune da iyalanmu. Idan gwamnati ta gano mu da wani laifi ai sai ta kama mu ta kai mu gaban shari’a, idan kuma har an same mu da laifi, sai a hukunta mu.