✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Musulunci ta tsare boka kan sace motar jaruma Fati Muhammad

Kotun Musulunci ta tsare boka bisa zargin sa da sace motar fitacciyar jarumar finafinan Hausa ta Kannywood, Fati Muhammad.

Babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano ta tsare wani boka bisa zargin sa da laifin satar motar fitacciyar jarumar finafinan Hausa ta Kannywood, Fati Muhammad.

Tunda farko ‘yan sanda ne suka gurfanar da bokan bisa zargin ya canza sunansa a wurinsu daga Isah zuwa Muhammad tare da hadin bakin wani mai suna Sulaiman Kiyawa suka yi wa jaruma Fati Muhammad dadin baki cewar an yi mata sammu, suka ba ta wani rubutu ta sha.

Takardar karar ta ci gaba da cewa bayan da jarumar ta kwankwadi rubutun ne hankalinta ya gushe, inda su kuma suka yi amfani da wannan damar suka sace mata mota.

Sai dai wadanda ake zargi sun musanta aikata laifin inda kuma suka nemi beli.

Alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da bayar da belin nasu bisa sharadin wani dagaci ko mai unguwa wanda Sarki ne ya nada shi ya tsaya musu.

Sannan a samu ma’aikacin gwamnati wanda ke matakin albashi na 15 wanda kuma ke da gida a Abuja.

Haka kuma sai an ajiye Naira miliyan biyu kwatankwacin rabin kudin motar jarumar da aka sace.

Daga baya alkalin ta sanya ranar 20 ga watan Yuni don ci gaba da sauraren shari’ar.