✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tabbatar da daurin shekara 10 ga Joshua Dariye

Ta tabbatar da laifin tsohon Gwamnan Filato na facaka da Naira biliyan 1.1

Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 10 a kan wani tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye.

Wani kwamitin alkalai mai mambobi biyar, baki daya ya amince da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja wacce a baya ta rage hukuncin daga daurin shekara 14 zuwa shekara 10.

Hukuncin wanda hukuncin da Mai Shari’a Ejembi Eko ya yanke, wanda mai shari’a Morenikeji Ogunwumiju ya karanta, ya goyi bayan hukuncin Babbar Kotun Abuja wacce a watan Yunin 2018 ta samu Dariye da aikata laifin cin amana.

Kwamitin, ya kuma soke hukuncin da aka yanke masa kan badakalar aikata laifin almubazaranci wanda aka rage zuwa shekara guda kuma wanda da zai yi ne a lokaci guda.

A shekarar 2007 ne EFCC ta tuhumi Dariye da laifuka 23 da suka hada da cin amana da kuma almubazzaranci da Naira biliyan 1.1 na Jihar a lokacin da yake kan mulki tsakanin 1999 da 2007.

Amma kotun da ke shari’ar ta same shi da laifi a kan laifuka 15 daga cikin 23, wadanda 11 daga cikinsu laifuka ne na cin amana da kuma hudu na aikata ba daidai ba tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.

Amma a Kotun Daukaka Kara, karkashin kwamitin alkalai da Mai Shari’a Stephen Adah ya jagoranta, ya rage wa’adin zuwa shekara 10.

Yanzu haka Dariye yana Gidan Yarin Kuje a Abuja, inda ya shafe kusan shekaru hudu a a daure.