Kotun Koli ta Najeriya ta rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN) guda 72 a safiyar Litinin.
Sai dai Shugaban Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Tanko, wanda shi ya kamata ya jagoranci taron bai halarta ba.
- ’Yan daba sun tsarwatsa taron samar da tsaro a Arewa
- Sojoji sun zagaye dajin da aka kai daliban da aka sace
- Dalibai 333 ne suka bace a GSSS Kankara —Masari
- Amurka ta tabbatar da yi mata kutse a shafukan intanet
Sakamakon haka alkali mafi girma a Kotun Koli, Mai Shari’aOlabode Bodes-Rhodes Vivour ce ta rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin a madadinsa.
An ba wa lauyoyin matsayin na SAN ne a matsayin shaidar gwanancewa a manazarta kuma masu kare hakki.
A watan Nuwamba ne Kwamitin Alfarmar Ayyukan Shari’a ya amince da daga martabar lauyoyi 72 zuwa matsayin SAN.
Da take ba su rantsuwa, Mai Shari’a Rhosdes-Vivour ta yi jan kunne ga masu saba wa umarnin kotu.
Bisa al’adar taron an shekara-shekara, Shugaban Alkalan Najeriya ne ke jagorantarsa; ba a samu bayanin dalilin rashin halartar Mai Shari’a Muhammad Tanko taron na 2020 ba.