✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotun Koli ta dakatar da aiwatar da wa’adin tsohuwar Naira

Kotun ta ce hukuncin da ta yanke na wucin-gadi ne.

Kotun Kolin Najeriya ta dakatar da Gwamnatin Tarayya daga aiwatar da wa’adin amfani da tsoffin takardun kudin kasar.

Hukuncin Kotun na zuwa ne bayan da Babban Bankin Najeriya CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsoffin takardun 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sauyawa fasali.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnoni uku ne dai da suka hadar da na Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da karar a gaban Kotun Kolin suna kalubalantar wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin.

A hukuncin wucin-gadin da suka suka yanke, alkalan kotun bakwai karshin jagaorancin Mai Shari’a John Okoro, sun dakatar da Gwamnatin Tarayya da CBN da sauran bankunan kasuwanci na kasar daga aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kudin kasar.

Kotun ta kuma ce dole ne Gwamnatin Tarayya da CBN da kuma sauran bankunan kasar su jingine batun aiwatar da wa’adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin ranar 15 ga watan Fabrairu.