✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta bai wa Amurkawa izinin yawo da bindiga

Kawo yanzu ana da akalla bindigogi miliyan casa’in da ke yawo a hannun Amurkawa.

Kotun Koli a Amurka ta zartas da hukuncin bai wa jama’a da shekarunsu na mallakar bindiga ya kai izinin yawo da bindigar don kare kai.

Wannan dai na zuwa ne a sabanin kiran da aka yi na tsaurara dokokin mallakar bindiga a kasar, inda tuni Shugaba Joe Biden ya bayyana takaici kan hukuncin kotun.

Ma’aikatar da ke kula da ’yancin masu mallakar makamai ta yaba da hukuncin da ya kawo karshen dambarwar da ta barke kan takaita hakkin mallakar makamai a baya-bayan nan a cikin kasar.

DW ya ruwaito cewa kawo yanzu ana da akalla bindigogi miliyan casa’in da ke yawo a hannun Amurkawa.

Dambarwar ta barke a baya-bayan nan a kasar kan takaita amfani da bindiga a sakamakon yawan harbin kan mai uwa da wabi da suka yi sanadiyar salwantar rayuka a sassan kasar.

Rahotanni sun gano cewa, an fi samun asarar rayuka ta hanyar amfani da bindigogi a Amurka fiye da rayukan da ke salwanta a tsakanin sojojin kasar da ke a fagen daga koma hatsarin mota da sauran iftala’i.