A yayin da ake ake sa ran Kotun Kolin Najeriya za ta yanke hukuncin karshe kan mutumin da ya yi nasara a zaben gwamna na jihar Kano, wasu ‘yan jam’iyyar PDP da Kwankwasiyya sun shaida wa Aminiya cewa suna da kwarin gwuiwa saboda hukuncin da kotun ta yi na baya-bayan nan.
Hukuncin da kotun za ta yanke tsakanin Gwamna Abdullahi Umare Ganduje na APC, wanda INEC ta sanar a matsayin wanda ya lashe zaben, da kuma Abba Kabir Yusuf na PDP, wanda ke kalabalantar nasar tasa, kusan shi ne ya fi jan hankalin jama’a.
Har ila yau a ranar Litinin din ne kotun, wadda Hausa ke cewa daga nan sai Allah Ya isa, za ta yanke hukunci kan zaben Sokoto tsakanin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na PDP da Ahmed Aliyu na APC.
Tuni dai rahotanni suka nuna cewa batun dakon hukuncin kotun shi ne lamarin da ya mamaye zukatan da dama daga cikin al’ummomin jihohin biyu.
Muna fatan samun adalci
A makon da ya gabata ne kotun ta soke zaben Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP sannan ta nada Hope Uzodinma na APC duk da cewa Iheordia ne ya yi nasara a kotuna biyu na farko.
“Wannan babu shakka ya karawa mutanenmu kwarin gwuiwa duk da cewa muma an ce ba mu yi nasara ba a kotuna biyun farko,” a cewar Barrister Maliki Kuliya wani jigo a PDP a Kano kuma jagora a tsagin Kwankwasiyya.
Mu dama kiran da muke yi shi ne abi dokar tsarin zabe, kuma indai an yi haka, to muna fatan samun nasara, a cewar lauyan, wanda na daya daga cikin masu kare jam’iyyar PDP.
Ana sa bangaren, Alhaji Suraja, jigo a Gidauniyar kwankwasiyya, ya shaida wa Aminiya cewa suna da “tabbacin insha Allah za mu samu adalci na kwatowa injiya Abba Kabir da jama’ar Kano hakkinsu”.
Ya kara da cewa shugaban Kotun Koli ya sha “alwashin tabbatar da adalci ba tare da nuna son kai ba kuma kotun ta bambanta da kananan kotuna, kuma abin da ya faru a shari’ar jihar Imo, ya nuna hakan”.
Sai dai yayin da ‘yan Kwankwasiyya ke cewa suna da gwarin gwuiwa, su ma magoya bayan gwamna Ganduje cewa suke yi ko gezau ba su yi ba, domin suna da yakinin su ne ke da nasara.
‘Yan Gandujiyya ko gezau
Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar Alhaji Murtala Sulen Garo, ya shaida wa wakilinmu a Kano cewa suna da kwarin guiwa kamar yadda “muka yi nasara a kotun farko da ta biyu, haka za mu yi a wannan ma insha Allah”.
Ya kara da cewa “sun shirya dukkan bayanansu kamar suka gabatar a shari’un da suka gabata, kuma suma ‘yan hamayya sun gabatar da nasu, don haka hukunci kawai ake jira kuma muna da nasara insha Allah”.
Haka shi ma wani magoyin bayan Gwamna Ganduje, Sani Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa “ko gezau ba mu yi domin kuwa insha Allah mu za mu yi nasara kamar yadda muka yi a baya”.
Aminiya ta fahimci cewa tuni Gwamna Ganduje da manyan jami’an gwamnatinsa suka shafe kwanaki a Abuja gabanin zaman kotun.
Su ma magoya bayan PDP da dama ne ake sa ran za su isa birnin na tarayya domin zaman kotun.
Ita dai jam’iyyar PDP da dan takararta Abba Kabir, wanda ke kan gaba a zaben farko da aka gudanar wanda bai kammala, kafin daga bisani Ganduje ya lashe bayan an kammala, sun shigar da kara ne suna kalubalantar zaben musamman matakin da hukumar zabe ta dauka na soke kuri’un da aka kada a mazabar Gama.
A Sokoto ma rashin kammala zaben a karon farko ne ya haifar da sake yin kwarya-kwaryar wani, sai dai Gwamna Tambuwal, wanda shi ne a kan gaba tun farko, shi ne ya lashe zaben da dan karamin rinjaye.
Bayanai sun nuna cewa duka magoya bayan bangarorin a jihohin na Kano da Sokoto sun dukufa wurin yin addu’o’i domin samun nasara.
Masu lura da al’amura na ganin watakila hukuncin kotun ya kawo karshen turka-turkar siyasar da aka shafe dogon lokaci ana yi a jihohin na Kano da Sokoto.