Kotun Daukaka Kara da ke birnin Kwatano na Jamhuriyar Benin ta ba da umarnin daure mai fafutukar kafa kasar Yarabawan nan, wato Sunday Igboho a gidan yari.
Sai dai kotun ta ki amincewa da bukatar tisa keyarsa zuwa Najeriya, yayin da zai ci gaba da zama a can har zuwa lokacin da za su kammala bincike.
Kotun, wacce ya kamata ta fara sauraron karar tun kusan karfe 10:00 na safiyar Litinin ta hana ’yan jarida da magoya bayan Igbohon shiga cikinta lokacin da ta fara zama da misalin karfe 5:00 na yamma.
Aminiya ta gano cewa daga bisani an tarwatsa magoya bayan nasa wadanda suka yi cincirindo a wajen kotun, suna tsoron za a iya tisa keyarshi zuwa Najeriya.
Gwamnatin Najeriya dai na zargin Igboho me da safarar makamai, tayar da zaune tsaye da kuma yunkurin ballewa.
Ta kuma bukaci a tiso mata keyarshi zuwa gida.
An dai kama Igboho tare da matarsa Ropo a Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Cardinal Bernardin a makon da ya gabata lokacin da suke kokarin sulalewa zuwa Jamus.
Amma a ranar Alhamis, kotun ta sallami matar, wacce ’yar asalin kasar Jamus ce yayin da shi kuma ta ba da umarnin tsare shi a kurkuku.
A ranar daya ga watan Yuli ne dai Hukumar Tsaro ta DSS ta ayyana Igboho a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bayan jami’anta sun yi dirar mikiya a gidansa da ke Ibadan, suka kashe biyu daga cikin yaransa sannan suka kama 12.