Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), ta ba da umurnin kamo Shugaban Rasha, Vladimir Putin saboda laifukan yaki da ake zargin ya aikata, wadanda suka hada da yin garkuwa da kananan yara.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Juma’ar, kotun ta ICC ta zargi Putin da laifin “kwashe wasu yara kanana daga yankunan da Rashar ta karbe iko a Ukraine ba bisa ka’ida ba, inda aka mayar da su Rasha.”
Kotun har ila yau, ta ba da iznin kama Kwamishiniyar Kare Hakkin Yara a ofishin shugaban kasar ta Rasha, Maria Alekseyevna Lvova Belova, wacce ita ma ake zargin ta da hannu a lamarin.
Sai dai ana ganin gurfanar da wani dan kasar Rasha a gaban kotun ta ICC, wani abu ne da zai zama mai kamar wuya, duba da cewa Rashar ba ta mika ’yan kasarta don su fuskanci hukunci a wata kasa.
A halin yanzu Rasha ba ta cikin mambobin ICC, abin da ya haifar da sarkakiya kan yadda kotun za ta matsa kaimi kan sammacin.
Tuni gwamnatin Rasha ta mayar da martani, tana bayyana wannan matakin na Kotun ICC a matsayin shirme.
Ita kuwa gwamnatin Ukraine ta yi jinjina ne ga kotun ta ICC, tana mai bayyana matakinta a matsayin wani sabon tarihi da aka kafa a tsarin shari’ar kasa da kasa.
A ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, dakarun Rasha suka fada wa Ukraine da yakin da kasashen duniya da dama suke Allah wadai da shi.
Daruruwan dubban mutane sun mutu tun bayan fara yakin yayin da aka tafka asarar dukiyoyi da dama.