✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Kotun ICC ta ba da umarnin kamo Fira Ministan Isra’ila

Kotun ICC na neman Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kan aikata laifukan yaƙi a Zirin Gaza

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ba da umarnin kamo Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da ministan kan laifukan yaƙi a Zirin Gaza.

Sauran waɗanda Kotun ICC ke neman su ne tsohon ministan tsaron Isra’ila da kuma jami’an kungiyar Falasɗinawa ta Hamas.

Laifukan sun hada da zargin kisan kiyashi a yankin Falasɗinu da kuma harin da kungiyar Hamas ta ƙaddamar a ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda a sakamakonsa ne Isra’ila ta far wa Zirin Gaza da hare-hare ta ko’ina.

Ƙasashe da kungiyoyi da dama ne dai suka maka Isra’ila a gaban kotun duniya (ICC) kan tauye haƙƙin ɗan Adam da kisan kiyashin da take wa Falasɗinawa da ke neman samun ƙasarsu mai cikakken ’yanci.

Sama da Falasdinawa 40,000 ne Isra’ila ta hallaka a Gaza cikin shekara guda, yawancinsu mata da ƙananan yara da kuma tsofaffi.

Yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza ya ɗaiɗaita rayuwar Falasɗinawa inda ta raba mutane kimanin miliyan biyu da muhallansu.

Baya ga lalata gidaje da ba za iya lissafa hakikanin adaddinsu, hare-haren sojojin Isra’ila a kan asibitoci da makarantu da wuraren ibada da kasuwanni da sansanonin gudun hijira da sauran wuraren taron jama’a a Gaza na ci gaba da ja mata tofin Allah tsine.