✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Daukaka Kara ta kori Gwamnan Jihar Filato

Kotun ta ce Gwamnan ya saba wa sashe na 177 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta soke zaben Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato.

Wani kwamiti alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Elfrieda Williams-Dawodu a wani mataki da ya yanke a ranar Lahadi, ya ce Muftwang ba cikakken dan jam’iyyar PDP ba ne.

Alƙalan sun ce ƙarar da ɗan takarar APC Nentawe Goshwe ya ɗaukaka ta yi nasara saboda batun tsayar da ɗan takara lamari ne da ya shafi lamurran kafin da kuma bayan zaɓe, saɓanin hukuncin da kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta bayar, inda ta bai wa Mista Muftwang nasara.

Tawagar alƙalan ta amince da mai ƙorafin (Goshwe) cewa gazawar PDP na gudanar da bin umarnin wata Kotun Filato da ya ce a gudanar da sahihan tarukan jam’iyya a mazaɓa da ƙananan hukumomi da kuma jiha kafin tsayar da ’yan takara ya saɓa wa doka.

Wannan dalilin ne ya sa kotun ta yi watsi da hukuncin kotun farko a matsayin “wanda bai dace ba kuma ya saɓa da yi wa kowane ɓangare adalci ta hanyar sauraron hujja daga shaidun da aka kora daga shari’ar.”

Kotun wadda ta soke hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da tabbatar da zaben Mutfwang, ta ce Gwamnan ya saba wa sashe na 177 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Kwamitin ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta baiwa Muftwang tare da ba Nentawe Goshwe na jam’iyyar APC sabuwar takardar shaidar lashe zabe.