Babbar Kotun yankunan Ingila da Wales a kasar Birtaniya ta yanke wa Attajiri mai harkar man fetur a Najeriya, Abdulrahman Bashir, mai kamfanin Rahamaniyya Oil & Gas, hukunci wata 10 a kurkuku.
Kotun ta kuma ci Rahamaniyya tarar fam dubu dari biyar (kimanin Naira niliyan 250) saboda kin bin umarnin kotu.
Shi kuma manajan kamfanin, Adebowale Aderemi, zai biya tarar fam 10,000, da ya yi daidai da Naira miliyan biyar a kudin Najeriya.
A watan Fabrairu, Mai Shari’a Butcher, ya zartar da hukuncin ne bisa kin yin biyayya ga umarnin da kotun ta ba shi a kan kararsa da kamfanin Sahara Energy Resources ya shigar.
“Dalilin wannan hukunci shi ne, Bashir ya saba wa umarnin Mai Shari’a Robin Knowles ranar 1 ga watan Agusta, 2019, da kuma umarnin da Mai Shari’a Justice Bryan ya ba shi a ranar 6 ga watan Satumba, 2019,” inji Butcher
Umarnin da kotun ta ba Rahamaniyya Oil and Gas Ltd, wadda Bashir ke shugabanta, shi ne, ya bayar da man gas adadin Metric tonnes 6,400.69 ga kamfanin Sahara Energy Resource Ltd.
Kotun kuma ta nuna yiwuwar za a iya rage hukuncin zuwa wata shida idan ya aiwatar da abun da kotun ta bukaci ya yi can baya.