Kotu ta yi watsi da ikirarin Abdulmalik Tanko ya yi cewa ba a cikin hayyacinsa ya fada mata cewa shi ne ya kashe dalibarsa mai shekara biyar, Hanifa Abubakar ba.
A yanzu haka kotun na shirin yanke hukunci kan Abdulmalik Tanko kan zargin kashe dalibar tasa wadda ya yi garkuwa da ita.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Usman Na’abba, zai yanke wa Abdulmalik Tanko hukunci ne bayan tabbatar da cewa babu wanda ya tursasa wanda ake zargin fadar cewa shi ya kashe ta a karon farko.
Tun da farko, Abdulmalik ya bukaci kotun ta yi watsi da bayanin da ya yi da farko, bisa hujjar cewa ya amsa cewa shi ne ya kashe Hanifa ne domin ya ceci ransa na a hannun ’yan sanda masu bincike.
Daga nan sai alkalin ya ba da umarnin sauraron batun halascin karbar jawabin nasa, a lokacin zaman.
Abdulmalkin ya bayyana a lokacin zaman cewa ’yan sanda masu bincike sun azabtar da shi tare da barazanar kashe shi idan bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.
Amma kuma matarsa, Fatima Jibrin, wadda ake zargin su tare, ta bayyana cewa masu binciken sun razana ta, amma ba su doke ta ba.
Sai dai masu binciken sun musanta zargin, suna masu cewa sun karbi bayanan wadadan ake zargin ne ta hanyoyi da bin ka’idojin da suka dace.
“Na gamsu cewa an karbi bayanan mutum biyu na farko da ake zargi ne da yardarsu, saboda haka an karbi bayaninsu,” inji alkalin.