✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ɗaure matashi kan wulaƙanta Naira a TikTok

Mai shari’a Aikawa ya yanke wa Muhammed hukuncin ɗaurin watanni shida (6) ko kuma ya biya tarar Naira dubu ɗari uku (₦300,000.00) ga Gwamnatin Tarayyar…

Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC reshen shiyyar Kaduna ta gurfanar da wani Muhammad Kabir a gaban kotu tare da yanke masa hukunci, wanda ya kasance mai wallafa bidiyo a shafukan TikTok da Instagram.

An gurfanar da Muhammad Kabir a gaban mai shari’a Rilwan Aikawa na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna bisa laifin wulaƙantawa da lalata takardun Naira.

An kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Tudun Wada, Jihar Kaduna saboda yin wani bidiyo a shafinsa na TikTok da Instagram @youngcee0066 yayin da yake watsa takardar Naira a ƙasa, yana tattake su yana magana da harshen Hausa da kuma tursasa EFCC ta zo ta kama shi a inda yake.

Daga nan ne aka kama shi da laifin karya dokar babban bankin Najeriya (CBN) da ta haramta cin zarafi da wulaƙanta Naira.

Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi masa, ya ce: “Kai Muhammad Kabir Sa’ad (da aka fi sani da  youngcee0066) a wani lokaci a shekarar 2025 a Kaduna da ke ƙarƙashin ikon wannan kotun mai girma, ka wulaƙanta Naira wanda ya saɓa ƙa’ida, ta hanyar tattaka takardun kuɗin Naira yayin da kake yin hoton bidiyo na sada zumunta da yaɗawa a intanet, sannan yin hakan aikata wani laifi ne na Babban Bankin Nijeriya na 2007 mai hukunci a ƙarƙashin Sashe na 21 (1) na wannan dokar.”

Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa lokacin da aka karanta masa, wanda hakan ya sa lauyan mai shigar da ƙara, M.U Gadaka ya roƙi kotu da ta yanke masa hukuncin da ya dace.

Sai dai Mai shari’a Aikawa ya yanke wa Muhammed hukuncin ɗaurin watanni shida (6) ko kuma ya biya tarar Naira dubu ɗari uku (₦300,000.00) ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya.