✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yi watsi da bukatar dakatar da babban taron APC

Kotu ta ce dan jam'iyya ba shi da hurumin maka jam'iyyar a gaban kotu

Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da aka shigar a gabanta na dakatar da babban taron jam’iyyar APC mai mulki.

Kotun ta ba wa jam’iyyar izinin ci gaba da shirye-shiryen taron da za ya gudanar ranar 26 ga Maris da muke ciki.

A zaman kotun na ranar Juma’a, alkalin kotun, Mai Shari’a Bello Kawu ya ce mamban jam’iyyar ba shi da hurumin kai karar jam’iyyar da yake ciki a gaban kotu.

Mai Shari’a Bello Kawu ya bayyana cewa umarnin kotu na ranar 18 ga watan Nuwamban 2021 da ya hana gudanar da taron ya zama tsohon labari.

Ya bayyana cewa hukuncin Kotun Koli na baya-bayan a kan irin wannan batu ya shafe umarnin kotun na watan Nuwamba.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Maris.