Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar Adamawa da ke zamanta a Yola, ta yi fatali da karar da ‘yar takarar APC a zaben Gwamnan da ya gabata, Sanata Aishatu Dahiru Binani ta shigar tana kalubalantar nasarar Gwamna Ahmed Umaru Fintiri.
Binani dai ta shigar da karar ce tana so kotu ta soke nasarar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce Fintiri na jam’iyyar PDP ya samu a zaben watan Maris din da ya gabata.
- Maharba sun kama mutum 4 da ake zargi da garkuwa da mutane a Taraba
- Ina addu’ar kada Allah Ya ba ni abin da mutane ba za su amfana ba — Alhaji Aminu Dantata
Sai dai da take yanke hukunci ranar Asabar, Mai Shari’a Theodora Uloho, ta ce masu karar sun gaza gabatar da kwararan hujjojin da za su tabbatar da da’awarsu cewa an saba wa Kundin Dokar Zabe ta Kasa ta 2022 a yayin zaben.
Fintiri dai ya lashe zaben ne da kuri’u 430,861, inda ya doke Binani mai kuri’a 398,788.
Idan za a iya tunawa, sai da aka je zagaye na biyu kafin a bayyana wanda ya lashe shi, saboda INEC ta ayyana na farko a matsayin wanda bai kammala ba.