Wata babbar kotu da ke zamanta a Kaduna, ta yi fatali da karar jagoran mabiya darikar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky yayin da kuma ta ba da umarnin a ci gaba da shari’ar da ke gabanta ta tuhumar da gwamnatin jihar ke yi masa.
An gurfanar da Sheikh Zakzaku da matarsa a gaban kotu kan tuhume-tuhume takwas na kisan kai, hada taron jama’a da ya saba wa doka, da kuma hargitsa zaman lafiyar al’umma da makamantansu.
- An yanke hukuncin kisa kan malamar da ta sa wa dalibai guba a abinci
- ’Yan sanda sun cafke mata da miji da kan mutum a Ogun
A safiyar jiya Litinin ne jagoran mabiya Shi’a ya nemi kotun da ta yi watsi da karar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar a kansu saboda abin da ya kira a matsayin rashin hujja.
Alkalin Kotun, Mai shari’a Gideon Kudafa, yay i watsi da bukatar Zakzaky tare da cewa bai gama sauraron gundarin karar da Gwamnatin Kaduna ta shigar ba ballatana ya yanke hukunci.
A dalilin haka ne Alkalin ya dage sauraron karar zuwa 18 da 19 ga watan Nuwamban 2020 domin ci gaba da shari’a da kuma ba wa lauyan da ya shiga da kara damar gabatar da shaidunsa a gaban kotu.
Tun a watan Dasumba na shekarar 2015 Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenatu ke tsare bayan wata mummunar arangama da mabiyansa suka da wata tawaga ta Rundunar Sojin Kasa a garin Zaria.