Wata kotu da ke zamanta a Jihar Legas ta yanke wa wani mutum, Ekpo Lawrence, mai shekara 42 hukuncin daurin rai da rai sakamakon samunsa da laifin yi wa ’yar cikinsa fyade.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Abiola Soladoye, ya yanke hukuncin ne bayan gabatar da hujojji da aka yi a gaban kotun wanda gwamnatin Jihar ke kararsa kan bata ’yar tasa mai shekara 15 a duniya.
Alkalin ya ce ya gamsu da shaidun da aka gabatar akan wanda ake zargin, sannan ya ki aminta da shaidun wanda ake zargin, inda ya ce hujojjinsu ba su da inganci.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin a gaban kotun.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar mai gabatar da kara a gaban kotun, Misis Bola Akinsete, ta ce laifin ya saba da sashe na 137 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015.
Kazalika, ta ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin tsakanin watan Disambar 2018 da Yunin 2019 a gidansa da ke unguwar Agege a Legas.
Yarinyar dai ta bayyana wa kotun yadda mahaifin nata ya ke lalata da ita a duk lokacin da mahaifiyar ta fita unguwa.