✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke wa soja hukuncin kisa ta haryar harbi

Kotun soji ta kama shi da laifin bindige kwamandansa da gangan a Borno

Kotun soji ta yanke wa sojanta da ya bude wa Kwamnadansa wuta ya kashe shi hukuncin kisa ta hanyar harbewa.

A zaman kotun sojin na ranar Talata, alkalan kotun sun kama Trooper Azunna Maduabuchi da laifin kashe bindige Laftanar Babakaka Ngorgi.

An gurfanar da kurtun sojan ne saboda bude wa Lafnar Babakaka Ngorgi wuta a kurkusa a watan Yulin 2020 a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno saboda Mataimakin Kwamandan nasa ya ki ba shi hutu ya je ya ga iyalansa.

An gurfanar da Maduabuchi ne a gaban kotun da ke zamanta a Barikin Sojoji na Maimalari da ke Maiduguri, tare da wasu sojoji hudu da ake zargi da aikata kisa.

Sauran sojojin da aka yanke wa hukuncin sun hada da Sajan Sani Ishaya wanda kotun ta yanke wa hukuncin daurin shekara hudu a kurkuku.

Ta kuma yanke wa Bidemi Fabiyi hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari yayin da Musa Bala da Abdulraheed Adamu kuma kowannensu aka yanke masa hukuncin daurin shekara daya a gidan jarun.

Kurtun soja ya bindige kwamnadansa

Aminiya ta kawo muku rahoton yadda kurtun sojan ya hallaka kwamandansa ta hanyar yi masa ruwan harsasai a Bama, Jihar Borno.

Sojan ya harbi Laftanar Babakaka Ngorgi sau takwas, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar hafsan.

Majiyarmu ta soji ta ce kurtun wanda nan take aka tsare shi ya dade yana hakon hafsan wanda suke aiki tare a Bataliyar Tankoki ta 202 a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Ta ce kurtun ya bude wa mamacin wuta ne ta baya kuma a kusa da shi, inda nan take ya rasu.

Majiyar ta ce a ‘yan shekarun an samu irin wannan matsalar tsakanin sojoji rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram a Gwoza, Chibok, Bama da kuma Mallam Fantori.

Mamacin ya kammala kwalejin kananan hafsoshi ta NDA ne a 2016, sannan ya yi aure watan Disamban 2019.