✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke wa matashi hukuncin bulala a Kano

Kotu ta sa a yi masa bulala bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa

Kotu a Jihar Kano ta yanke wa  wani matashi hukuncin bulala tare da biyan tarar Naira 10,000 kowannensu.

Kotun Majistaren ta yanke hukuncin ne bayan ta kama matashin mai shekaru 25 da laifin sayar da miyagun kwayoyi, addabar al’umma da kuma mallakar sholisho da sukudaye masu gusar da hankali.

Bayan Mai Shari’a Farouk Ibrahim ya karanto masa laifin da ake tuhumarsa, sai ya matashin amsa da cewa ya aikata.

Da yake yi wa kotun jawabi, Mai gabatar da kara, Lamido Soron-Dinki, ya ce an kama wanda ake zargin ne a lokacin wani samame da suka kai a Karamar Hukumar Fagge ta Jihar Kano.