Wata Babbar Kotu mai zamanta a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, ta yanke wa wasu mutum hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A ranar Litinin Kotun ta yanke hukuncin bayan da ta samu matasan da aikata laifin fashi da makami da yukurin kisa da sauransu.
- Majalisa ta ba NNPC mako daya ya kawo karshen wahalar mai a Najeriya
- NAJERIYA A YAU: IPOB Ko Gwamnati: Wa Ke Iko Da Kudancin Najeriya?
Wadanda lamarin ya shafa, dukkansu matasa ne ‘yan shekara tsakanin 22 da 23.
Tun a watan Agustna 2020 aka gurfanar da masu kare kansu a gaban Mai Shari’a Bamidele Omotoso, kan tuhumar laifuka bakwai ciki har da fashi da makami da hadin baki da sauransu.
Laifukan da kotun ta ce sun saba wa sassa na 516 da 402(2) da 320 na Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Ekiti na 2012.
Domin gamsar da Kotun, mai tuhuma, Albert Adeyemi, ya gabatar wa kotun shaidu shida tare da sauran bayanai da kuma makaman da aka kwace a hannun masu laifin.
Mai Shari’a Omotoso ya ce, ya yanke wa masu kare kansu hukuncin kisa ta raya ne bayan da kotu ta kama su da aikata laifukan da aka tuhume su.
Ya kara da cewa, kisa shi ne hukuncin laifin fashi da makami, hakan ya sa aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta yanke musu hukuncin daurin rai da rai saboda laifin yukurin kisa, sannan daurin shekara bakwai ga kowannensu kan laifin hadin baki.