Wata Babbar Kotun Jihar Osun da ke Osogbo fadar jihar ta yanke wa wasu mutum biyar da ta samu da laifin garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta yanke musu hukuncin ne bayan samunsu da laifin sace wani makiyayi mai suna Alhaji Ibrahim Adamu, tare da kashe shi.
An gurfanar da mutum biyar ɗin ne a gaban alƙali bisa tuhume-tuhumen da suka ƙunshi haɗa baki don yin garkuwa da mutumin da laifin kisan kai, zargin da suka musanta a lokacin da aka fara gurfanar da su ranar 28 ga Oktoban 2021.
A lokacin sauraron shari’ar, lauyan gwamnati, Faremi Moses, ya gabatar da hujjojin da ke nuna cewa mutanen sun yi garkuwa da Alhaji Ibrahim Adamu a ranar 17 ga watan Afrilun 2018 a gidansa da ke Ƙaramar Hukumar Ede ta Arewa a Jihar Ogun.
Lauyan ya ce mutanen sun kashe Alhaji Ibrahim Adamu bayan iyalansa sun biya kuɗin fansa Naira miliyan uku.
Lauyan waɗanda ake zargi ya ce hujojjojin mai gabatar da ƙara ba su da ƙarfin da za su iya gamsar da kotu.
Sai dai lokacin da take yanke hukunci, Mai shari’a, Kudirat Akano ta ce kotu ta samu mutum biyar ɗin da laifuffuka huɗu, inda ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.