Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Lakwaja ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin daurin shekara 36 saboda laifin garkuwa da mutane da mallakar makami ba bisa ka’ida ba.
A zaman kotun na ranar Alhamis, Mai shari’a P.Mallong, ya yanke wa na farkon hukuncin daurin shekara 20, na biyun kuma shekara 16.
- Manyan motoci sun tare hanyar Abuja kan rufe masana’antar Dangote
- Rashin Man Fetur ya tashi hankalin masu motoci a Faransa
An kama na farkon ne da wata bindiga kirar gida a kauyen Ofara, aka gurfanar da shi a bisa zargin aikata laifuka biyar.
Mai shari’a P.Mallong ya yanke masa hukuncin daurin shekara 4 kan kowanne daga tuhume-tuhumen biyar da aka yi masa, watau shekara 20 a jimla ce.
Daga cikin laifukan, kotun ta same shi da laifin yin garkuwa da wata mata na tsawon kwanaki, har sai da ’yan banga da wasu jami’an tsaro suka kubuto ta.
Tun da farko, jami’in rundunar DSS mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu guda hudu da wasu hujjoji da kotun ta karba a matsayin madogara.
Dayan wanda aka tuhuma da laifukan hadin baki da ta’addanci da kuma garkuwa da mutane kuma, alkalin ya yanke mishi hukuncin jimlar shekara 16 a gidan yari.