A farkon makon nan ne wata Babbar Kotu a birnin Bombay na Indiya ta wanke jarumin fim, Gobinda daga laifin marin da ake tuhumarsa da aikatawa tun a 2008. Santosh Rai ne dai ya shigar da karar shekaru biyar da suka gabata, inda ya zargi jarumin da marinsa da kuma yi masa karfa-karfa.
Mai shari’a M. L. Tahaliyani ne ya wanke Gobinda daga laifin, inda ya bayyana cewa babu wata shaida ta zahiri da ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, don haka kotu ba za ta iya kama shi da laifi ba.
Rai ne dai a ranar 2 ga Fabrairun 2009, ya shigar da kara a gaban kotun Majistare, inda ya tuhumi cewa Gobinda ya ci zarafinsa da mari da zagi da nufin harzuka shi, kawai saboda ya ziyarci wurin da suke daukar shirin fim a ranar 16 ga Janairun 2008.
Shi kuwa Gobinda sai ya garzaya Babbar Kotu, inda ya nemi da a warware wannan tuhuma da ake masa a kotun Majistare.
“Tun da farko ma, bai kamata kotun baya ta saurari karar ba, a karkashin sashi na 323 da 504, domin kuwa an shigar da karar ne bayan shekara daya cur da aikata laifin da ake zargi. Idan aka yi la’akari da sashi na 506 (1) kuwa, kotun farko ya kamata ta nazarci cewa ko akwai tabbatattar shaidar da za ta tabbatar da laifin ko babu.” Inji mai shari’a Tahaliyani, a yayin da yake sallamar Gobinda.
Haka kuma, Babbar Kotun ta yi la’akari da rahoton ’yan sanda, wanda ya nuna cewa al’amarin mari da cin zarafin, ba a bayyana shi karara ba kamar yadda mai kara ya fada. “Babu shakka kam wani abu ya faru amma duk da haka babu tabbatattar shaidar da za ta gamsar da aikata laifin. Al’amarin dai ya nuna cewa an shirya wa mai karar giri ne, ya amince ya shigar da karar.” Inji kotu.
Kotun kuma ta yi la’akari da cewa wanda ake tuhuma bai yi wani abu da har ya jaza a yi kararsa ba. “Irin wannan shari’a, bai kamata a bari ta ci gaba da gudana ba, don haka ya dace a kore ta.” A cewar mai shari’a Tahaliyani.