✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta wanke Babachir daga zargin badakalar N544m

Mai Shari’a Charles Agbaza ya ce duka shaidu 11 da EFCC ta gabatar babu wanda ya nuna laifin da aka aikata.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sallami tare da wanke tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, kan zargin badakalar kwangilar Naira miliyan N544.

Kotu ta wanke Lawal ne tare da wasu mutum biyar bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da su.

A ranar Juma’a Kotun ta yanke hukunci cewa an kayar da EFCC a shari’ar bayan ta gaza gamsar da kotu da hujjoji.

A ranar Litinin, 30 ga Nuwamba, 2020 EFCC ta sake gurfanar da Babachir Lawal a gaban Alkali Justice Agbaza.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Charles Agbaza ya ce duka shaidu 11 da EFCC ta gabatar wa kotu babu wanda ya nuna laifin da aka aikata.

Akalin ya ce babu inda EFCC ta nuna Babachir Lawal mamba ne a bangaren gwamnatin da ya ba da kwangilar, ko kuma mamba a bangren da ya bincika kafin amincewa da ba da kwangilar da ake batu a shiyyar Arewa maso Gabas.

EFCC na tuhumar Babachir Lawal ne tare da kaninsa Hamidu Lawal da Suleiman Abubakar da Apeh Monday da kuma wasu kamfanoni biyu.

Ana tuhumarsu ne da yin sama-da-fadi da kudaden kwangila miliyan N544 na kwangilar da aka kuduri aiwatarwa a yankin Arewa maso Gabas.