Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta wanke Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Aminu Bashir Wali daga zargin karkatar da Naira miliyan 950.
Kotun ta wanke Ambasada Wali ne tare da tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Mansur Ahmad da ake tuhumar su da kwanciyar magirbi da kudaden yakin neman zaben 2011.
- Yadda Kanawa 16 suka mutu a hatsarin mota a Kaduna
- ‘Yadda auren dana zai kasance da matar sa Ba’amurikiya’
- Karamar yarinya ta mutu a rijiya a Kano
- Yadda rashin tsaro ya sa ’yan Arewa dawowa daga rakiyar Buhari
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da su bisa zargin karbar kudaden ba tare da bin ta banki ba, sabanin dokar safarar da haramtattun kudade ta 2011.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Lewis Allagoa ya ce bangaren masu gabatar da kara sun kasa tabbatar da zargin da suke yi.
Don haka ya yi fatali da karar hukumar ya kuma wanke wadandada ake zargin.
Ambasada Wali ta bakin lauyansa, Sam Olagunorisa ya ce sun ji dadin wankewar da kotun ta yi musu, ya kuma kara da cewa kudaden da ake zargi sun bi da hannun halastacciyar cibiyar kudi.
Lauyan EFCC, Cosmos Ogwu, a nasa bangaren, ya ce maganar ta kare, tun da dama shari’a sabanin hankali ce.
Sai dai ya ce: “Za mu kara nazarin hukuncin mu ga abin da za mu iya yi daga baya”.