✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci MTN ya biya mawaki diyyar N20m

Kotun dai ta sami MTN da laifin satar fasaha

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci kamfanin sadarwa na MTN ya biya wani mawaki, Liberty Williams, wanda aka fi sani da Papayannis Naira miliyan 20 saboda yi masa satar fasaha.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa mawakin mazaunin Abuja a wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/2017 da ya shigar a shekarar 2017 ya maka MTN da shugaban kamfanin, Ferdi Moolman da kamfanin Nowhere to Run Entertainment Ltd da kuma Emmanuel Abanah, a gaban kotun.

Da take yanke hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce MTN ya karya dokar hakkin mallakar wakar mawakin mai suna “Love is Everything”, inda ta ce ba su da hurumin yin amfani da ita ba tare da izininsa ba.

Ta kuma dakatar da kamfanin da sauran wadanda ake karar daga ci gaba da amfani da wakar.

Alkalin ta kuma umarci kamfanin da ya cire wakar ta Papayannis daga jerin wakokin da ake ji idan aka kira masu amfani da layin.

Lauyan mai kara, Mabruk Kunmi-Olayinka ya ce wadanda ake karar sun gaza kawo gamsassun hujjojin da za su nuna ba satar fasahar wakar suka yi ba.

Mawakin dai ya bukaci kotun da ta ayyana yadda MTN ya yi amfani da wakarsa a matsayin caller tune kuma yake karbar kudi a kaI ba tare da izininsa ba, a matsayin satar fasaha. (NAN)