✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci INEC ta bar PDP ta duba kayayyakin zaben Kano

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe da ke Jihar Kano ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sahale wa dan takarar Gwamna na…

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe da ke Jihar Kano ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sahale wa dan takarar Gwamna na Jama’iyyar PDP Alhaji Abba Kabir Yusuf damar duba kayayyakin zabe da aka yi amfani da su a zaben Gwamnan Jihar Kano da aka gudanar a a ranakun 9 da kuma 23 ga watan Maris da ya gabata.

Kotun ta yi wannan umarni ne bayan rokon da Jam’iyyar PDP ta yi ta bakin lauyanta Barista Maliki Kuliya Umar inda ya shigar da wata bukata gaban kotun a ranar 4 ga Afrilun nan yana nemi a sa Hukumar INEC ta ba dan takarar damar duba dukkan kayayyakin da aka yi amfani da su a lokutan zaben.

Daga cikin bukatun da lauyan ya gabatar gaban kotun sun hada da ba Abba Kabir Yusuf na Jma’iyyar PDP damar duba takardun sakamakon zabe da takardun kada kuri’a da na’urar tantance masu zabe wadanda aka yi amfani da su a lokacin zaben.

Da take yanke hukunci kotun ta amince wa dan takarar dukkan bukatun da ya nema, haka kuma kotun ta amince wa Jam’iyyar APC da ta bayar da wakilai biyu ko uku daga bangarenta da za su sanya ido a lokacin duba kayayyakin zaben.

Shi dai wanda ya kai karar Abba Kabir Yusuf da Jam’iyyar PDP suna kalubalantar Hukumar INEC da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje game da hanyoyin da aka bi wajen zaben tare da bayyana Gwamnan a matsayin wanda ya lashe zaben  jihar.