Babbar Kotun Taryya da ke Abuja ta ce tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai iya zuwa Kano a duk lokacin da ya ga dama, kuma korarsa daga Jihar da gwamnati ta yi take hakkinsa ne na ’yancin watayawa.
Kotun, ta kuma umarci Gwamnatin Jihar Kano da Babban Sufeton ’Yan Sanda da Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya (SSS) da su biya shi tarar Naira miliyan 10, sannan su ba shi hakuri a cikin akalla jaridu guda biyu.
- Kotu ta rushe tsagin Ganduje na shugabancin APC a Kano
- Pogba ya soma tattaunawa da PSG, Modric zai koma City
Da take yanke hukuncin ranar Talata, Alkalin kotun, Mai Shari’a Anwuli Chikere, ta ce hanyar da aka bi wajen fitar da tsohon Sarkin ta karfin tsiya zuwa Jihar Nasarawa bayan cire shi daga sarauta bai dace ba.
Ta kuma ce matakin na Gwamnatocin Jihar Kano da Nasarawa da hukumar SSS na fitar da shi ba bisa san ransa ba, take hakkinsa ne a matsayinsa na dan Adam.
Alkalin ta kuma ce sabuwar Dokar Masarautu ta Jihar ta Shekarar 2019, wacce gwamnatin ta yi amfani da ita wajen daukar matakin haramtacciya ce.
Mai Shari’a Anwuli, ta kuma ce a matsayinsa na dan Najeriya, Sanusi bai aikata kowanne laifi ba, kuma yana da ’yancin zama a kowanne bangare na Najeriya, ciki kuwa har da Kano.
A watan Maris din shekara ta 2019 ne dai Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cire Sanusi II daga matsayinsa na Sarkin Kano na 14.
Bayan cire shin kuma, an fitar da shi daga Jihar zuwa garuruwan Loko da Awe na Jihar Nasarawa, kafin daga baya ya kalubalanci matakin a kotu, wacce ita kuma ta ba shi damar komawa Jihar Legas, kamar yadda ya bukata.
A al’adance dai a baya, idan aka cire Sarki daga sarauta, a kan haramta masa sake shiga garin har karshen rayuwarsa.