✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci EFCC da DSS da ’yan sanda su kamo Diezani 

Babbar Kotun Tarayya  da ke Abuja ta umarci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da Hukumar Tsaron Kasa ta Farin Kaya (DSS)…

Babbar Kotun Tarayya  da ke Abuja ta umarci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da Hukumar Tsaron Kasa ta Farin Kaya (DSS) da ’yan sanda umarnin su kamo  tare da gurfanar da Tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke  cikin awa 72 a kan zargin cin hanci da rashawa.

Wata sanarwa da  Kakakin Hukumar EFCC, Tony Orilade ya fitar a  ranar Talatar da ta gabata, ta ce kotun ta bayar da umarnin ne lokacin da alkalin kotun Mai shari’a Balintine Ashi ta yanke hukunci kan bukatar da Hukumar EFCC ta gabatar gaban kotun ta neman a ba ta izinin gurfanar da tsohuwar ministar a ranar Litinin ita da tsohon shugaban kamfanin mai na Atlantic Energy Drilling Company, Jide Omokore kan zargin aikata laifuffuka biyar.

EFCC na zargin su biyun da karbar hanci da kyaututtuka a wurare biyu a Legas, lamarin da ya saba wa dokar hana karbar hanci da rashawa.

Kotun ta umarci Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu da Sufeto Janar na ’Yan sanda da Ministan Shari’a da Daraktan Hukumar DSS su hanzarta kamo tsohuwar ministar. Hukumar EFCC ta shaida wa kotun cewa ta dade tana aike wa tsohuwar ministar takardar gayyata zuwa Najeriya domin ta kare kanta  kan zarge-zargen cin hanci da ake yi mata amma ta ki amsawa.

EFCC ta ce tsohuwar ministar ta bar Najeriya zuwa Ingila ne a lokacin da ake tsakiyar bincike kan zargin da ake yi mata.