Mai shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da ta bai wa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu damar ganin likitan da ya ke so.
Kotun ta riki hakan ne bisa bukatar da jagoran masu fafutikar na neman a yi masa tiyatar kunne cikin gaggawa sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.
Da take yanke hukunci, Mai shari’a Nyako, ta kuma umurci ’yan sandan na farin kaya da su kuma sanya ido, tare da tattara bayanan da suka danganci lafiyar jagoran na IPOB, domin dalilai na tsaro.
Alkalin kotun ta kuma yi watsi da karar farko da hukumar DSS ta shigar na kalubalantar bukatar da ke gabanta, da ke cewa Kanu na da hakkin duba lafiyarsa ko da a tsare.
Kotun, a hukuncin da ta yanke, ta kuma bayar da umarnin a ba da dukkan bayanan lafiyar Kanu ga shugaban kungiyar ta IPOB.
Kanu, wanda ke hannun hukumar DSS tun a watan Yunin 2021, yana fuskantar tuhume-tuhume masu alaka da ta’addanci da kuma cin amanar kasa.