✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Bauchi ta cire Saraki shida

Gwamnatin jihar Bauchi ta warware rawanin masu sarautun gargajiya guda shida bisa samunsu da laifin saɓa wa dokokin aiki. Hukumar kula da ma’aikatan ƙanann hukumomi…

Gwamnatin jihar Bauchi ta warware rawanin masu sarautun gargajiya guda shida bisa samunsu da laifin saɓa wa dokokin aiki.

Hukumar kula da ma’aikatan ƙanann hukumomi ce ta sallame su bayan samunsa da ‘tsoma kai cikin harkokin siyasa’ da kuma wasu laifuffukan na dabam.

Sarakin da aka sauke sun haɗa da Alhaji Aminu Muhammad Malami, Hakimin  Udubo, Alhaji Bashir Kabir Umar, Hakimin  Azare, Umar Omar, Dagacin  Gadiya, da Umar Bani Dagacin Tamasawa  duk a Masarautar Katagum.

Gwamnan Bauchi ya jagoranci Sallar rokon ruwa

Majalisar Dokokin Bauchi za ta fara amfani da Hausa a yayin zamanta

Daga Masarautar Bauchi kuma akwai Bello Sulaiman, Dagacin Beni da Alhaji Yusuf Aliyu Badara, Dagacin Badara.

Muƙaddashin babban sakataren hukumar, Nasiru Ibrahim ne ya sanar da sauke masu sarautun gargajiyar.

Sanarwar ta umarci waɗanda aka  sauke su miƙa takardun ajiye mulki ga sakatarorinsu kuma ta buƙaci masarautun da abin ya shafa su naɗa waɗanda za su kula da yankunansu kafin hukumar ta naɗa sababbi.