Mai dakin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta ce yanzu haka shekarunta na haihuwa sun kai 60, don haka ta yi tsufan da ba ta tsoron mutuwa.
Remi Tinubu ta bayyana hakan ne a Fadar Sarkin Bauchi, Dokta Rilwani Suleiman Adamu ranar Talata, kan wani bidiyon barazanar kisa da wani malami Sunusi Abubakar ya yi mata a kwanakin baya.
- Ɓangaren Lafiya Na Cikin Mummunan Yanayi A Gwamnatin Tinubu — Likitoci
- Ramadan: Hisbah ta kama marasa Azumi 12 a Kano
Remi ta kai ziyara jihar ne domin kaddamar da aikin makaranta da cibiyar horaswa kan fasahar bayanai da gwamnati ta yi a jihar.
A kwanakin baya ne dai bidiyon ya karade soshiyal midiya, inda malamin ya ce ya kamata a kawar da ita daga doron kasa, kafin daga bisani ya janye kalamansa bayan shan suka daga mutane.
“Ina son mika godiya ga Gwamna saboda tabbatar da rayuwata bata cikin hadari. Amma abin da zan ce shi ne na yi tsufan da bana tsoron mutuwa.
“Yanzu haka shekaruna 60, ba na jin ya kamata a ce ma na ji tsoronta. Duk da haka na gode Allah da na samu kwarin guiwar zuwa duk da waccan barazanar.
“Najeriya ta mu ce gaba daya, ya dace mu hada kai a yanzu fiye da a baya,” in ji Remi Tinubu.
Tun da fari dai Gwamnan Jihar Bala Muhammad ya nemi afuwar mai dakin shugaban a madadin ilahirin al’ummar jihar bisa waccan barazanar da aka yi mata a baya.