✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci a biya Sowere diyyar kamensa kan zanga-zangar juyin juya hali

Lauyoyinsa sun ayyana hukuncin a matsayin bayyanar gaskiya karara.

Babbar Kotun Tarayya ta umarci Hukumar DSS ta biya mawallafin Jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowere diyyar kamensa saboda assasa zanga-zangar juyin juya hali ta Revolution Now.

Kotu da ke Abuja yayin zamanta na ranar Talata, ta ayyana kamen da aka yi wa Sowore a matsayin haramtacce, tana bukatar biyansa diyyar abin da ta kira cin zarafin da aka yi masa.

Wannan dai na zuwa ne makonni uku bayan da wata Babbar Kotun a Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Chikere Anwuli ta umarci rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta biya Sowore naira miliyan biyu sakamakon karbe masa wayar hannunsa a yayin kamensa.

A hukuncin kotun, alkalin ya kuma ba da umarnin a saki wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu wajen mara wa Sowore baya a zanga-zangar tasa da ya yi wa lakabi da #RevolutionNow.

Tuni dai lauyoyin Sowore, Marshar Abubakar da Femi Falana suka ayyana hukuncin a matsayin bayyanar gaskiya karara kuma abin kunya ga hukumar tsaron sirrin kasar ta DSS.

A cewar lauyoyin, karara ya ke a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya cewa kowanne mutum na da ’yancin gudanar da zanga-zanga matukar ba za ta sauya zuwa tarzoma ba, kuma sun yi imanin wannan shi ne abinda wanda su ke karewa ya yi.

An dai kama Omoyele Sowere ne tun a ranar 3 ga watan Agustan 2019, sakamakon zarginsa da shirya wata mummunar zanga-zangar juyin juya hali mai taken “#RevolutionNow”.