Wata kotun Musulunci ta tisa ƙeyar wani alƙalin bogi zuwa gidan yari a Jihar Kano.
Dubun alƙalin bogin ta cika ne bayan da ya gabatar da kansa a matsayin alkali daga Jihar Jigawa a gaban Kotun Musulunci da ke unguwar Kurma, Ƙaramar Hukumar Fagge.
Asirin alƙalin bogin ya tonu ne a lokacin da ya je kotun neman belin wasu mutane biyu wadanda ake zargi da laifin damfara da cin amana.
Kotun ta amince da ba shi belin mutanen ne a bisa sharaɗin sai ya kai jami’an kotu gidansa, amma nan take ya ƙi amincewa.
- Auren Jinsi: Majalisa na neman a gaggauta binciken Sheikh Gadon Ƙaya
- Ƙarin Kuɗin Fetur: Hauhawar farashin kaya na iya ƙaruwa —MAN
Da aka tsananta bincike daga baya sai aka gano cewa ungulu da kan zabi ya yi, ma’aikacin shari’a ne, amma bai taɓa zama alkali ba.
A lokacin da aka gurfanar da shi, ya amsa laifinsa, sannan ya roki alkali ya yi masa sassauci.
Khadi Umar Lawan Abubakar ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari zuwa ranar 23 ga watan Satumba, 2024 domin ci gaba da shari’ar.