Kotun Majistare da ke zamanta a Chediya GRA, Zariya ta tsare wasu mutum biyar saboda tuhumarsu da hadin baki da aikata miyagun laifuka.
Laifukan sun hada da na niyyar kisan kai da raunatawa da kuma yin zagon kasa ta hanyar hana jami’an gwamnati gudanar da aikinsu wanda ya saba wa dokokin Jihar Kaduna.
Dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Abdullahi Rilwanu ya shaida wa kotun cewa a watan Mayu, Alkali Lamido Abubakar na Kotun Chediya GRA Zariya ya kai kara ofishin shiyya na ‘yan sanda a Zariya.
Ya ce Lamido ya zargi wasu mutum biyar mazauna Marabar Gwanda sun farmake su shi da ma’aikatan da ke taimaka masa wajen hukunta masu saba dokar kulle da gwamnatin Jihar Kaduna ta saka.
Ya ce a farmakin ya samu rauni a yatsarsa da kafarsa tare da bata wani bangare na mortar da suke aiki da ita a lokacin da suke zaman kotun tafi-da-gidanka a Marabar Gwanda.
Da yake bayyana matsayin kotu, Mai Shari’a Mustapha Dahiru Isah ya ce tuhumar da ake yi musu mai karfi ce na yunkurin aikata kisan kai.
Ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren karar don haka ya mika bayanan shari’ar ga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna don bayar da shawara kafin ranar 9 ga watan Satumba 2020 da za a sake zama.