Wata kotun Majistare da ke zamanta a birnin Osogbo, Jihar Osun ta tsare wani matashi a gidan yari kan zargin shi da daba wa makwabcinsa wuka.
Matashin, mai kimanin shekaru 23 dai an zarge shi ne da yankan makwabcin nasa a gidan haya.
- Hukuncin kisa zai hau masu satar mutane a Filato
- Mai ’ya’ya 8 na neman a raba aurenta na shekaru 19 saboda rashin abinci
Dan sanda mai shigar da kara, Olayiwola Razza ya shaida wa kotun cewa da gangan wanda ake zargin ya yi amfani da wuka wajen yi wa makwabcin nasa raunin a hannunsa na dama.
Ya ce yanzu haka dayan mai suna Dauda na can a asibiti yana ci gaba da samun kulawa.
A cewar dan sandan, mutanen biyu mazauna gidan haya ne guda daya.
Ya kara da cewa an aikata laifin ne da misalin karfe 8:30 na daren 24 ga watan Janairun 2021 a yankin Fiwasaye na birnin Osogbo.
Olayiwola ya ce laifin ya saba da tanade-tanaden sashe na 335 na kundin manyan laifuffuka na Jihar Osun na shekarar 2002.
Lauyan wanda ake kara, Okobe Najite ya roki kotun da ta bayar da belin shi, yana mai ba da tabbacin cewa zai bayar da hadin kai a shari’ar.
Sai dai alkalin kotun, Mai Shari’a Ishola Omishade ya umarci a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari sannan ya dage zaman kotun zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu, 2021.