✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matashi a kurkuku kan zargin fyade

Matashin ya rudi yarinyar zuwa dakinsa ne a kan ta je ta karbi kudin kayan da ya saya a shagonsu.

Wata kotu a Jihar Kaduna ta ba da umarnin tsare wani matashi a gidan gyaran hali kan zargin yi wa ’yar makwabcinsa fyade.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Chidi Leo, ya fada wa kotun ranar Alhamis cewa, wanda ake zargin ya je shagon su yarinyar mai shekara 14 ce ya yi sayayya sannan ya bukaci ta bi shi ta karbi kudin, ganin cewa makwabta suke.

Ya ce, da isarsu, “Sai ya kama kofar dakinsa ya rufe sannan ya yi mata fyade.”

Lamarin da ya ce ya auku a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya ki amincewa da rokon da matashin ya yi wa kotun, inda ya ba da umarnin a kai shi kurkuku sannan ya dage shari’ar zuwa watan Janairu.

(NAN).