Wata Kotun Majistare ta Dutse a Jihar Jigawa ta tura wadansu matasa biyar da ke kauyan Diginsa a Karamar Hukumar Birniwa a jihar zuwa gidan kurkuku bisa zarginsu da yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyade.
Yarinyar wadda ta samu ciki bayan fyaden iyayenta ne suka kai korafi ga ’yan sanda, inda su kuma bayan bincike
suka kama wadanda ake zargin tare da su gabatar da su a gaban kotun.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Muhammad Haruna da Alhaji Maigawa da Adamu Haruna da Ciroma Muhammed da sai kuma Jibril Idris wanda ya musanta aikata laifin.
Alkalin Kotun Mai shari’a Usman Lamin ya umarci a tsare matasan na mako biyu a gidan yari na Garu kafin ci gaba da shari ar kamar yadda yake kunshe a karkashin sashi na 282 na kundin manyan laifuffuka na Jihar Jigawa
A wata sabuwa kuma an gurfanar da wani matashi mai suna Badamasi Barde a gaban kotun bisa zargin boye wata budurwa har kwana 39 a wani wuri da ba a sani ba. Matashin dan Unguwar Gyadi Gyadi da ke Kano ana zargi ya boye budurwar mai suna Farida Yahuza ’yar Unguwar Jigawar Sarki da ke garin Dutse fadar Jihar Jigawa.
Ma’aikatan Hukumar Sibil Difens ne suka gano inda matashin ya boye budurwar a cikin watan azumin da ya gabata.
Kuma wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa a gaban kotun, inda Mai shari’a Usman Lamin ya tura shi gidan maza zuwa ranar 24/7/2017 domin ci gaba da shari’arsa.