Kotu ta tsare wasu mutane a gidan yari saboda zaman hira a wata majalisar da suka kirkira da ke addabar mutanen unguwa.
Kotun Majistaren ta tsare mutanen su takwas ne saboda laifin tayar da zaune tsaye, cikin har da wata dattijuwa mai shekara 51 da ta kirkiri zaman hirar.
- Kotu ta daure tsohon Shugaban FaransaNicolas Sarkozy
- Yajin Aiki: DSS ta gayyaci shugaban dillalan shanu da kayan abinci
Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Adebayo Joseph, ya ce majalisar hirar da dattijuwar da abokan hirarta suka kafa ba ka’ida ba bisa ka’ida ba, ta hana makwabta sakat.
ASP Adebayo, ya shaida wa kotun masu majalisar hirar sun aikata laifin ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar 24 ga watan Fabrairun 2021 a yankin Enuwa da ke Ile-Ife, na Jihar Osun.
Sauran mutum bakwai din da kotun ta tsare a zamanta na ranra Litinin sun hada da matasa masu shekara 20, 23, 25, 26, 27, 34 da kuma 45.
Ya ce abin da wadana ake zargin suka aikata laifi ne karkashin 70, 249(d) da 517 na kundin dokokin hukunta manyan laifuka na Jihar Osun na shekarar 2002.
Sai dai wanda ake zargin sun musanta aiakta laifuka uku da ake tuhumar aikatawa na tayar da zaune tsaye.
Lauyan wadanda ake zargi, Philip Fasanmoye, ya bukaci belin su tare da alkawarin cika sharudan belin da kuma gabatar wa da kotun wadanda za su tsaya musu a shari’ar.
Amma alkalin Kotun, Mai shari’a, A. A. Adebayo ya ki amincewa ya kuma bayar da umarnin ci gaba da tsare su a Gidan Kurkuku na Ilesa saboda hakan ya zama darasi ga na baya.
Adebayo, ya dage zaman Kotun zuwa ranar 22, ga watan maris na shekarar 2021 don ci gaba da sauraren karar.