Wata kotun Abuja mai zamanta a yankin Karu, ta ba da umarnin tsare wasu masu gadi su biyu a gidan yari kan zargin satar katifun makaranta guda 69.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Umar Mayana, wanda ya ba da umarnin hakan ranar Laraba, ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Disamba.
- Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano
- Bata-gari sun kwakule idon almajiri a Bauchi
Tun farko, lauya mai gabatar da kara, Olarewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa mai karar wanda babban jami’i ne a wata makarantar Abuja, ya kai rahoton batun ofishin ‘yan sanda da ke Kurudu.
Mai tuhumar ya ce masu kare kansu sun saci babban talabijin inci 32 da katifun makaranta guda 69 wanda a kiyasce kudin kayan ya kai Naira miliyan uku da dubu dari daya.
“Yayin binciken ‘yan sanda, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu,” in ji Osho.
Haka nan, ya ce, laifin da suka aikata ya saba da sassa na 97 da 289 na kundin Penal Code.
(NAN)