A ranar Talata wata Kotun Shari’a da ke Kano, ta ba da umarnin adana wani magidanci a gidan Dan Kande bisa zargin yin garkuwa da wata tsohuwar matarsa wadda a yanzu take aure da wani daban.
Magidancin wanda mazaunin Karamar Hukumar Ganjuwa a Jihar Bauchi ne, ana tuhumarsa da laifin garkuwa da kuma kulla alaka da matar aure.
- An rufe Coci saboda sayar da ‘maganin bindiga’ a Kogi
- An ceto mutum 7 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
Tun farko lauyan mai tuhuma, Aliyu Abideen, ya shaida wa kotu cewa mijin matar, Alhaji Amadu Yahuza daga Karamar Hukumar Kunchi ta Jihar Kano, ya kai karar batun ofishin ’yan sanda na yankin Gama da ke Kanon a ranar 13 ga Satumba.
Yahuza ya yi ikirarin cewa wanda ake zargin ya kira matarsa a waya wani lokaci a cikin watan Agusta a kan ta zo ta same shi a garin Ganjuwa da ke Jihar Bauchi.
Ya kara da cewa, “Wanda ake zargin ya aika wa tsohuwar matar tasa da kudin mota sannan bayan ta kai kanta, ya kai ta zuwa wani wuri da ba a sani ba a Jihar Bauchi.”
A cewar mai tuhumar, yayin da ake bincike an gano wayar matar a hannun wanda ake karar.
Kodayake, wanda ake tuhama ya musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa.
Lauya Abideen ya fada wa kotun cewar, laifin ya saba wa sassa na 270 da 312 na kundin dokokin shari’ar Jihar Kano.
Kazalika, Alkalin kotun Malam Nura Yusuf-Ahmad ya dage sauraron shari’ar zuwa 29 ga Satumba, 2022 tare da ba da umarnin ajiye wanda ake zargi a gidan gyaran hali.
(NAN)