✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare magidanci kan gwada ƙarfi a kan matarsa a Kano

Matar ta shigar da ƙara ne kan yadda mijin nata ke gwada ƙwanjinsa a kanta.

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Filin Hockey a Unguwar Hausawa a Jihar Kano, ta tsare wani magidanci mai suna, Abdullahi Muhammad, a gidan gyaran hali bisa zargin sa da gwada ƙarfi da tsoratar da matarsa.

Tunda farko matar ta kai ƙarar mijin ofishin ’yan sanda na Gwale kan cin zarafinta da kuma lakaɗa mata dukan kawo wuƙaz wanda ya kai da ta samu rauni.

Mai gabatar da ƙara, Barista Muhammad Dandago, ya karanta wa wanda ake ƙara tuhumar da akemasa, amma ya musanta aikata laifin.

Lauyan da ke kare mijin matar a gaban kotun, Barista Umar I. Umar, ya nemi kotun ta bayar da belinsa dogaro da sashe na 36 na kundin tsarin mulkin ƙasa.

Sai dai mai gabatar da ƙara, Barista Muhammad Dandago, ya yi suka kan roƙon lauyan wanda ake zargi.

Mai Shari’a Abdullahi Halliru, ya aike da shi ajiye a gidan gyaran hali har zuwa ranar 14 ga watan Yuni, 2024,