Kotun Lardi ta Birnin Tarayya da ke garin Jiwa a Abuja, ta bada umarnin a tsare wani direba mai shekara 36 mai suna Samson Boje kan zargin yi wa agolarsa ciki, bayan rasuwar mahaifiyarta.
Lauyan masu shigar da kara na Gwamnatin Tarayya mai suna Uche Uchegbulam a ranar Litinin da ta gabata ya shaida wa kotun cewa bayan rasuwar mahaifin yarinyar, mahaifiyarta ta auri mutumin, amma sai ita ma Allah Ya karbi rayuwarta a watan Disamban shekarar 2013.
Ya ce a watan Yunin bana ne yarinyar ta taso daga gidan wani baffanta inda take zaune a wani yanki na Abuja don ziyartar kanwarta mai shekara 6 da mahaifiyarta ta haifa a gidan wanda ake zargin, amma sai ya shaida mata cewa yarinyar ba ta nan, sai dai ta sake dawowa wata rana, kamar yadda ya yi bayani.
Sai dai a cewarsa bayan yarinyar ta sake komawa gidan sai mutumin ya rike ta sannan a karshe ya yi mata fyade da ya kai ta ga samun ciki da ya kai wata 4 a yanzu.
Da alkali ya waiwayi wanda ake zargin ya musanta tuhumar. Daga nan ne sai lauyansa mai suna C.C. Nwankwo ya bukaci a bada belinsa. Sai dai alkali ya ce a ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan batun bayan lauyan masu kara ya bukaci haka.