Wata kotu a Makurdi, Jihar Binuwai, ta ba da umarnin tsare wani magidanci mai shekaru 45, bisa zargin sayar da ’yarsa mai shekaru hudu kan Naira miliyan 20.
’Yan Sanda sun kamo mahaifin yarinyar ne tare da abokinsa, bisa zarginsu da aikata laifin hadin baki da sata da safarar karamar yarinya.
- Rasha za ta bai wa Afghanistan Man Fetur da Alkama na shekara 1
- Ambaliya ta ci mutum 3, wasu 50,000 sun rasa muhallansu a Kogi
Alkalin kotun dai ta ba da umarnin tsare su a gidan kaso na Makurdin, tare da dage sauraren karar zuwa ranar 1 ga watan Disamba.
Tun da farko ’yar Sanda mai gabatar da kara, Insfekta Veronica Shaagee, ta ce sakamakon rahoton sirri da suka samu ne suka kamo mutanen, aka tsare su a sashen binciken manyan laifuka da ke Makurdi.
An dai kama magidancin da abokinsa ne suna tsaka da cinikin yarinar, sai dai wanda ake zargin zai saye ta ya cika wandonsa da iska.
Laifin da Shaagee ta ce ya sabawa sashe na 97 na kundin Penal Code na Jihar Binuwai na 2004, da sashe na 3(2) na dokar hana satar dan Adam na 2017, da na 2006 19 (1).