✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta takadar da Giadom daga jam’iyyar APC

Kotu ta dakatar da Mataimakin Babban Sakataren Jam’iyyar APC da aka dakatar, Victor Giadom daga dukkan harkokin jam’iyyar. Babbar Kotun Jihar Ribas, mahaifar Giadom ta…

Kotu ta dakatar da Mataimakin Babban Sakataren Jam’iyyar APC da aka dakatar, Victor Giadom daga dukkan harkokin jam’iyyar.

Babbar Kotun Jihar Ribas, mahaifar Giadom ta bayar da hukuncin ne washegarin ranar da Majalisar Zartarwar Jam’iyyar APC na Jihar Ribas ta dakatar da shi. Reshen jam’iyyar ya kuma gabatar wa uwar jam’iyyar da Worgu Boms ya maye gurbin Giadom, kuma jam’iyyar ta rantsar da Boms din a ranar Litinin.

A hukuncin da aka yanke, Mai shari’a C. Nwogu na Babbar Kotun Jihar Ribas Mahaifar Giadom, ya ce, “An bayar da umurni na wucin gadi da ke hana wanda ake kara na uku [Giadom] daga gabatar da kansa a matsayin jami’i ko dan jam’iyya… ko kuma cin gajiyar duk wani hakki ko alfarmar da ‘yan jam’iyya ke da ita.

Tun a ranar Litinin dama wata kotu ta dakatar da Giadom daga gabatar da kansa a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa na wucin-gadi, mukamin da ya nada kansa bayan Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta dakatar da Shugaban Jam’iyyar na Kasa Adams Oshiomhole daga shugabancin jam’iyyar.

Nada kansa da Giadom ya yi a matsayin shugaban riko sabanin Prince Hilliarda Eta da jam’iyyar ta nada, ya sa shugabannin jam’iyyar APC dakatar da Giadom din bisa zarginsa da zubar da kimar jam’iyyar.

A hukuncin kotun, Mai Sharia C. Nwogu ya ce, tunda har Majalisar Zartarwar Jihar ta dakatar da shi, to Giadom kar ya sake ya shiga harkokin jam’iyyar har sai kotun ta gama sauraron shari’ar.

Hukuncin na zuwa ne a sharia’ar karar da Okechukwu Chidor Ogbonna da kuma Mac-Lords Peterson suka shigar suna karar jam’iyyar APC; shugabanta na riko a jihar Ribas, Igo Aguma; Victor Giadom da kuma Golden Chioma.

Kotun ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Yuli.