✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta soke daukar ’yan sanda 10,000 da aka yi a 2019

Kotun Daukaka Kara ta soke daukar kurata 10,000 da Shugaban na ’Yan Sandan Najeriya ya yi a 2019

Kotun Daukaka Kara ta soke daukar kurata 10,000 da Shugaban na ’Yan Sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu ya yi a bara.

Kotun ta ce sassan Dokar Aikin Dan Danda ta 2020 da aka yi amfani da su wajen daukar kuratan ya saba ka’ida.

Ta ce sassan sun yi karo da tsarin mulkin kasa da ya ba Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda (PSC) alhakin daukar duk wani ma’aikaci a Rundunar ’Yan Sanda, banda ofishin IGP.

Idan za a iya tunawa Hukumar ta yi karar IGP a gaban Babbar Kotun Abuja, kan daukar kurata 10,000 da ya yi bisa sahalewar Shugaba Buhari.

Bayan kotun ta yi watsi da karar ne hukumar ta je Kotun Daukaka Kara inda Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce Kwamitin Manyan ’Yan Sanda da IGP ke jagoranta ne ke da hurumin daukar kurata aiki.

Kakakin PSC, Ikechukwu Ani, ya ce kotun ta ce sassan Dokar Aikin Dan Sandan da aka yi amfani da su wurin daukar kuratan sun saba wa damar da tsarin mulki kasa ta ba su.

“Dokar ta 2020 ta ci karo da Sakin layi na 30, Sashe na 1 na Kudin Tsarin Mulki na 1999 da ya ba PSC hurumin daukar ma’aikata a dukkannin ofisoshi banda na IGP”, inji Ani.

Ya ce cikakken bayanin na kushe ne a takardar hukuncin kotun da hukumar ta karba a watan Satumba, 2020.