✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke belin abokin tuhumar tsohon Akanta-Janar Ahmed Idris

Ana zargin tsohon Akanta-Janar din da almundahanar Naira biliyan 109.5

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta soke belin da a baya aka bai wa abokin tuhumar tsohon Akanta-Janar na Kasa, Ahmed Idris.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Yusuf Halili ne ya yanke hukuncin da cewa an soke belin  wanda ake tuhuma a shari’ar da ake musu bisa zargin karkatar da kudaden baitul mali har Naira biliyan 109.5.

Bayanai sun ce alkalin kotun ya soke belin Geoffrey Olusegun Akindele, biyo bayan rashin bayyanarsa a kotu domin ci gaba da shari’ar.

Akindele, wanda shi ne wanda ake tuhuma na biyu a shari’ar mai lamba CR/199/2022, da kuma tsohon Akanta-Janar Idris suna fuskantar tuhume-tuhume tare da Mohammed Kudu Usman da Kasuwar Musayar Kayayyaki da ke Gezawa.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa, ta maka su kara ne a gaban kotu kan tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata, da almundahana da dukiyar al’umma zuwa Naira biliyan 109.5.

EFCC ta yi zargin cewa ta haka ne suka aikata laifin da ya saba wa sashe na 155 na dokar Penal Code Act Cap 533 na Dokokin Tarayyar Najeriya na 1990 da kuma hukunta su a karkashin wannan sashe.

A ci gaba da sauraron karar a yau Talata, Mista Akindele bai halarci kotun ba har zuwa lokacin da ake sauraron karar, duk da cewa Idris da Usman suna gaban kotun.

Duk da rokon da lauyan Mista Akindele, S.E. Adino ya yi na cewa wanda yake karewa yana kan hanyar zuwa kotu, inda ya gabatar da cewa shi (Akindele) yana kasancewa a kotu ko da yaushe domin fuskantar shari’a, Mai shari’a Halilu ya dage kan soke belin wanda ake kara na biyu.

Daga nan sai ya dage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 1 ga watan Fabrairun 2024.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Yulin bara ne dai wata Babbar Kotun Abuja da ke zamanta a unguwar Maitama ta bayar da belin tsohon Akanta Janar na Tarayyar.

Wannan dai ya zo ne mako guda bayan da kotu ta tasa keyar tsohon Akanta Janar din zuwa gidan dan Kande bayan umarnin da ta bayar na ci gaba da tsare shi tare da wadanda ake tuhuma a gidan yari na Kuje har sai an saurari bukatar neman belinsu.