✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Zamfara ya ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi

Gwamnan ya ayyana dokar ne ganin yadda ilimi ke tafiyar hawainiya a jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya ayyana dokar ta baci kan harkokin ilimi a jihar.

A wani jawabi da gwamnan ya yi a ranar Talata, ya ce tsarin ilimi da aka yi watsi da shi a Zamfara ya shafi duka matakai tun daga firamare zuwa manyan makarantu, da rashin muhallin karatu da ma’aikata.

Cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi ya yi daidai da alkawuran yakin neman zaben Lawal.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin na kokarin yin garambawul a fannin ilimi wanda daf yake da durkushewa.

Sanarwar ta kara da cewa: “A wani sako a yau, Gwamna Dauda Lawal ya ayyana dokar ta baci a fannin ilimi a fadin Jihar Zamfara.

“Hakan ya yi daidai da tsarin yakin neman zabensa, inda ya yi wa al’ummar Zamfara alkawarin aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin gyara fannin ilimi.

“Saboda haka, gwamnatin Dauda Lawal ta fara bayar da agajin gaggawa kamar haka: gine-gine da gyara makarantu 245 a fadin kananan hukumomi 14 na jihar; samar da tebura masu kujeru biyu ga dalibai, ga makarantu 9,542 a kananan hukumomi 14; kayan aiki, gyara makarantu 245 da sauran su.

“Za a bai wa malamai horo na musamman game da harkokin ilimi.

“Don tabbatar ingancin ilimi, gwamnati ta dakatar da lasisin makarantu masu zaman kansu a jihar. Wannan wani mataki ne na kokarin tabbatar da bin ka’idoji ga makarantun.

“Bugu da kari, domin samar da ilimi mai inganci, gwamnatina ta amince da daukar nauyin karatun kashi 50 na ’yan asalin Jihar Zamfara zuwa Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Gusau don yin karatu a shekarar 2023 zuwa 2024.

“Gwamnati ta biya Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) kudin jarabawa ga duk ‘yan asalin Jihar Zamfara da suka zana jarabawar 2023.

“Daliban da aka rike sakamakon jarabawarsu a baya saboda rashin biyan kudin NECO, yanzu haka mun biya kuma za su iya mallakar sakamakon jarabawar tasu.

“Gwamna Lawal ya biya kudin karatu da alawus-alawus na dalibai a kasashe daban-daban da suka hada da Sudan, Cyprus, da Indiya. Hakan ya tabbatar da cewa za su ci gaba da karatunsu ba tare da tangarda ba saboda basukan da gwamnatin baya ta ci.

“Gwamnati ta kuduri aniyar sauya yanayin rashin aikin yi. Zamfara za ta ci gaba a kowane fanni. Wannan shi ne mafarin aikinmu.”